fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Duminsa: ‘Yan Bindiga sun kashe jama’ar gari, sojoji da ‘yansanda 20 a mummunan harin da suka kai Erena jihar Naija

Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba inda ‘yan Bindigar suka kai harin da misalin karfe 2 na dare.

 

Sun budewa ‘yansanda da sojoji wuta suka kashe su sannan sun kuma kashe wani dan kasar China da wasu masu hakar zinare.

 

Hakanan sun yi garkuwa da mutane a harin.

 

Wani mazaunin garin Erena da Hutudole ya zanta dashi ya shaida mana cewa sojoji 3 ne aka kashe sai ‘yansanda 7.

“Jiya Mopol 7
Soja 3 A yanzu Kuma Maganar Danakeyi Dakai Wani Yadawo Daga Gurin Yace Gwa 20 Yanani”

Karanta wannan  Naira miliyan 650 masu garkuwa da mutane suka samu a cikin shekara guda-Bincike

 

Zuwa yanzu dai hukumomi basu ce komai ba kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.