‘Yan Bindiga wanda ake zargin ‘yan Kungiyar Asiri ne sun yiwa wani DPO din ‘yansanda me suna Bako Angbashim yankan Rago.
Lamarin ya farune a Ahoada dake karamar hukumar Ahoada a jihar Rivers.
An kasheshine a daren ranar Juma’a.
Bidiyon kanshi da mazakutarshi da hannayensa sun bayyana inda aka ga an musu daidai.
Hukumar ‘yansandan jihar ta tabbatar da kisan.
Bayan da ‘yan Bindigar suka dauke DPO din dai, an sake kawo sojoji da sauran jami’an tsaro wanda zasu kwato gawarshi, amma suka kasa shiga inda ‘yan Bindigar suke inda suka ce gurin yayi duhu da yawa.