fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Da Duminsa: Yan Ta’adda Sun Sake Kai Hari Garin Gujba na Jihar Yobe

Yan ta’addan Boko Haram a ranar Asabar sun kai hari garin Gujba na karamar hukumar Gujba na jihar Yobe.
Wannan harin ya zo ne kwanaki biyu bayan da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari a kan al’ummar Geidam da ke jihar inda suka kona shaguna tare da kwashe magunguna.
Da yake magana da gidan talabijin na Channels, wata majiya a yankin, Adamu Bura, ta ce ‘yan ta’addan sun fara yin kwanton bauna ne a kan wata motar sintiri ta sojoji a kan babbar hanyar sannan daga baya suka afka wa kauyen suka kone wasu gine-gine.
“Sun yi kwanton bauna a motar sojoji sannan daga baya suka wuce zuwa garin Gujba. Mun gudu zuwa daji amma muna ganin hayaki ko’ina, ”inji shi.
Ita ma rundunar ‘yan sanda reshen jihar Yobe ta tabbatar da kai harin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, ASP Dungus Abdulkarim, ya ce har yanzu bayanai game da wadanda suka rasa rayukansu ba a tabbatar ba.
Amma kokarin da aka yi na jin ta bakin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na sashin 2 na Operation Lafiya Dole, Laftanar Kennedy Anyanwu, abin ya ci tura.
Duk da cewa kwanciyar hankali ya dawo yankin, har yanzu hukumomi ba su bayyana adadin wadanda suka rasa rayukansu da kuma dukiyoyin da suka lalace ba.
A makon da ya gabata ne, Shugaban Sojoj, Manjo Janar Nuhu Angbazo ya kaddamar da wani shiri na “Tura Takai Bango” a Bunigari don magance matsalar ‘yan ta’addan da suka addabi yankin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Har yanzu akwai sauran fasinjoji 27 a hannun 'yan bindiga, cewar Tukur Mamu

Leave a Reply

Your email address will not be published.