Majalisar wakilai ta kasar Amurka ta tsige shugaban kasa, Donald Trump daga mukaminsa a karo na 2.
Wannan yasa ya zama shugaban kasar Amurka na farko da aka tsige har sau biyu a tarihin kasar. Kusan duka ‘yan jama’iyyun dake majalisar sun amince da tsige Trump din ba tare da nuna banbanci ba.
An tsige Trump ne bisa zargin ya tunzura magoya bayansa auka kaiwa ginin majalisar, Capitol hari a ranar 6 ga watan Janairu.