A daren yau Talata, Sanata Kwankwaso ya sake kai wata ziyarar bazata gidan Sanata Shekarau da ke Unguwar Mundubawa dukda dai cikin shirye-shiryen Shekarau na ficewa daga APC zuwa Jam’iyyar NNPP.
Yanzu haka Sanata Shekarau ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar APC a hukumance, ya kuma umarci magoya bayansa da ke fadin Jihar Kano da su garzaya su yanki katin shaidar zama ‘ya’yan Jam’iyyar NNPP daga yau gobe Laraba.
A gobe Laraba 18, ga watan Mayun 2022 ake saran Sanata Shekarau zai gudanar da gangamin magoya bayansa da misalin karfe goma na safe a gidansa da ke Mundubawa, Kano.
Karanta wannan Bidiyo: 'Yan Achaba a kasar Kamaru na zanga-zangar vire tallafin man fetur a Najeriya
Idan hali ya yi zamu zo da karin bayani kan ziyarar Kwankwaso zuwa fadar Mundubawa.