fbpx
Friday, July 1
Shadow

Da Duminsa:Abubakar Shekau ya saki Sabon Bidiyo inda yayi wata sabuwar Barzanar kai hari

Boko Haram, bangaren Abubakar Shekau ta saki Sabon Bidiyo inda take ikirarin itace ta kai harin Toumour dake yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar da ya kashe mutane 27.

 

Harin ya farune a tsakanin ranekun Asabar da Lahadi inda wani jami’in Gwamnati a yankin ya bayyanashi da cewa wanda bai kamata bane kuma me hadari.

 

A harin, Boko Haram ta kone kaso 60 cikin 100 na gari  inda akalla gidaje 1000 suka kone da kuma kasuwar garin.

 

Harin ya farune a lokacin da kasar ke gudanar da zabuka amma sanarwar da Boko Haram din ta fitar tace harin bashi da alaka da zaben da ake, saidai zasu ci gaba da kai hare-hare, musamman yayin da Kirsimeti ke kara kusantowa, kamar yanda wakilin HumAngle  Aliyu Dahiru ya ruwaito.

Karanta wannan  Ji yanda sojojin Najariya suka kone gaba dayan wani kauye bayan da matasan kauyen suka kashe soja

“To all the Christians in the world, especially that Christmas is approaching, you should know we will never stop killing you,” he threatened.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.