Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Wase ya bayyana cewa a garinsu an kama soja da ya kamata ace yana Zamfara amma yana baiwa ‘yan Bindiga aron kayansa na aiki.
Yace an kama sojan aka mikashi ga hukumar sojoji kuma har yanzu basu ji labarin yanda aka yanke masa hukunci ba.
Yace ana ta baiwa Sojan damar zuwa ganin gida har na tsawon wata shida wanda hakan alamar tambayace.
Yace kuma an sake kama wani sojan da makamai a dai garin nasa.
Yace mutanen da ake maganar an kashe a jihar Filato sun fi haka, Allah ne kadai yasan yawansu dan kuwa har yanzu ana dauko gawarwaki daidai a daji.
Ya bayyana hakane a zaman majalisar yayin da suka tattauna matsalar tsaro.
A karshe dai sun nemi shugaba Buhari yawa bangaren tsaro garambawul