Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa wani lauya, Mr. Johnmary Jideobi Ya shigar da tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar kara a kotun tarayya inda yake neman a hanashi takarar shugaban kasa.
Yace Atikun ba dan Najeriya bane.
Hakan na zuwane bayan da Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.
Lauyan yace yana kuma karar PDP da hukumar zabe me zaman kanta, INEC, da kuma babban lauyan gwamnati.