Wani tela da ya bayyana goyon bayan dan siyasat da yawa Annabi Muhammad (SAW) batanci a kasar Indiya ya bakuncin Lahira.
Wasu masu kishin addinin islama ne dai suka yiwa Telan yankan rago.
Lamarin ya faru a Udaifur inda kuma suka dauki bidiyon irin kisan da sukawa telan.
Wanda suka yi kisan sun kuma nuna kansu inda sukace sune ke da alhakin kashe wanda yayi batancin.
‘Yar siyasar da ta yi wannan kalaman batancin dai tuni aka dakatar da ita.