fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Da Duminsa:ASUU, reshen jihar Filato ta tafi yajin aikin sai abinda hali yayi

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU, reshen jihar Filato ta tafi yajin aikin sai abinda hali yayi.

 

Malaman suna neman a inganta musu tsarin aiki da kuma kula da hakkokinsu.

 

Shugaban kungiyar da sakatarenta a jihar, Dr. Hassan Zitta da Deme Bitrus ne suka bayyana haka inda suka kara da cewa sun cimma wannan matsaya ne bayan taron da suka yi ranar 20 ga watan Disamba 2021.

 

Sun bayyana cewa, gwamnatin jihar Filato ta kasa biya mata alkawuran data dauka shiyasa suka dauki wannan mataki.

Leave a Reply

Your email address will not be published.