Bayan wadanda ta tura kasar Guinea Bissau su sama da 100, Najeriya zata sake tura wasu karin sojoji kasar Gambia dan samar da zaman lafiya.
Sojoji 197 ne za’a aika kasar ta Gambia wanda zasu yi aiki a karkashin kungiyar hadin kan kasashen Africa ta yamma watau, ECOWAS.
Jami’in sojin, Maj.-Gen. Olufemi Akinjobi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis.
Yace daga shekarar 1960 zuwa yanzu, Najeriya ta yi aikin samar da zaman lafiya a kasashe 40.