fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Da Duminsa:Dan Kunar bakin wake ya tayar da bam din daya jikkata mutane da sojoji

Rahotanni sun ce wani ɗan ƙunar bakin wake ya kai hari kan ababan hawan da ke wajen binciken motoci a babbar hanyar zuwa filin jirgin saman Aden Adde.

Wasu majiyoyi daga wajen da lamarin ya faru sun ce harin ya raunata mutane da dama ciki har da sojoji da fararen hula.

Wajen da aka kai harin na da nisan kilomita biyar ne daga filin jirgin saman, kuma anan ne ake ganin ‘yan takarar shugabancin kasar za su gudanar da jawabai a game da takararsu.

Karanta wannan  Yanda aka yi jana'izar matar da Inyamurai 'yan Bindiga suka kashe tare da 'ya'yanta

Tuni aka sanya dokar takaita zirga-zirga a wuraren da za a gudanar da zaben shugaban kasa a Ranar Lahadi mai zuwa.

‘Yan takara 39 ne ke neman kujerar shugabancin kasar wanda aka jinkirta shi saboda yanayin tsaro a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.