fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Da Duminsa:Hotunan dake nuna A’isha Buhari na da ciki na karyane>>Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta yi martani kan hotunan uwar gidan shugaban kasar, Hajiya A’isha Buhari da suka watsu inda aka rika cewa tana da ciki.

Hotunan sun dauki hankula sosai akaita bayyana mabanbanta ra’ayoyi akansu.

Saidai kakakin matar shugaban kasar, Sulaiman Haruna ya karyata wannan magana inda yace hotunan ba na gaskiya bane an musu siddabaru.

Haruna ya bayyana cewa, hotunan ba na gaskiya bane kuma matar shugaban kasar bata da ciki kuma lafiyarta kalau.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a BBC Pidgin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.