Wasu mutane da ake zargin IPOB ne sun kona wata motar dake dauke da shanu a kudu maso gabashin Najeriya.
Lamarin ya farune a ranar Lahadi kuma an ga bidiyon na yawo a shafukan sada zumunta.
An ga yanda shanu ke ta yawo a titi bayan kona motar.
Lamarin ya farune a Ezinifite/Uga dake karamar hukumar Aguata a jihar Anambra da misalin karfe 8 na ranar Lahadi.