fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Da Duminsa:Kotu ta hana jam’iyyar PDP shiga zaben Gwamna a jihar Zamfara

Kotun gwamnatin tarayya dake Gusau ta soke zaben dan takarar gwamna na jihar Zamfara, Dauda Lawan-Dare, inda kuma tace ba za’ mayeshi da wani dan takarar ba.

 

Mai shari’a, Aminu Bappa ne ya yanke wannan hukunci ranar Talata. Inda yace jam’iyyar PDP ba zata fitar da wani dan takarar ba a zaben 2023.

 

Wannan ne karo na biyu da kotu ke soke ‘yan takarar gwamna na jihar ta Zamfara.

 

Koda a watan Satumba da ya gabata, sai da kotun ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar ta PDP a jihar.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *