fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Da Duminsa:Mahaifin Tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso ya rasu

Allah Ya yi wa Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano da ke Najeriya kuma fitaccen dan siyasa Rabi’u Musa Kwankwaso, rasuwa.

Ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a yana da shekara 93 a duniya, a cewar sanarwar da Muhammad Inuwa Ali, wani mai babban hadimin tsohon gwamnan ya fitar.

Ya rasu ne a Kano.

Za a yi jana’izar Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, wanda ke rike da sarautar Majidadin Kano/Makaman Karaye, a yau Juma’a da misalin karfe uku na rana a gidan dansa da ke Miller Road a Bompai da ke birnin Kano.

Sanarwar ta yi kira ga jama’a su yi masa addu’a a maimakon hakan.

Marigayin ya bar mata biyu da ‘ya’ya 19 (mata 10, maza 9) da jikoki da dama.

A cikinsu har da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamna kuma tsohon Sanata, wanda shi ne jagoran Kwankwasiyya a jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.