fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Da Duminsa:Majalisa ta amince da dokar hana biyan ‘yan Bindiga kudin fansa

Kudirin dokar da ya hana biyan kudin fansa ga ‘yan Bindiga ya tsallake matakin karatu na 3 a majalisar dattijai.

 

Majalisar ta amince da kudirin bayan da dan majalisar, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da shi a zauren majalisar.

 

Sanatan ya bayyana cewa, dokar zata rage yawan garkuwa da mutane da ake yi.

 

Shima kakakin majalisar, Ahmad Lawal ya bayyana cewa, amincewa da dokar zata kawo saukin matsalar tsaron da ake fama da ita.

 

Ya kara da cewa, gwamnati ta yi ayyukan ci gaba sosai a kasar nan amma matsalar tsaro ta shafe wadannan ayyukan bama a ganin amfaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.