fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Duminsa:Majalisa tace matsalar tsaro ta yi yawa, shugaba Buhari ya tsige Ministan tsaro da mai bashi shawara kan tsaro

Majalisar wakilai ta nemi shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya sauke ministan tsaro, Bashir Magashi, da mai bashi shawara kan tsaro, Babagana Monguno.

 

Majalisar ta koka da cewa, matsalar tsaron Najeriya ta yi yawa suna mamakin me yasa shugaban kasar har yanzu yake tare da me bashi shawara kan tsaro bai canjashiba?

 

An samu munanan hare-hare a Najeriya da suka hada da kaiwa jirgin kasa me jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja hari da kashe wasu a ciki da sace wasu wanda har yanzu suna hannun ‘yan Bindigar.

Karanta wannan  Jesus ya fara bugawa Arsenal wasa da kafar dama inda yaci mata kwallaye biyu ta lallasa Lecester City 4-2

 

Akwai kuma harin da aka kai kan filin jirgin sama na Kaduna.

 

Hakanan akwai harin da aka kai garin Kanam na jihar Filato wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 150.

 

A baya dai an rika korafin cewa shugaban kasar ya canja Shuwagabannin tsaro na soji wanda kuma yayi hakan amma duk da haka za’a iya cewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.