Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar APC ta jihar Legas.
Hakan ya fito daga bakin kakakinsa, Laolu Akande a hirarsa da jaridar Independent.
Akande ya gayaaa jaridar cewa, Osinbajo tuni ya bar jam’iyyar APC din ta jihar Legas inda ya koma jihar Ogun.
Ana tunanin dai Osinbajon yayi hakane dan kauracewa rikici tsakaninsa da me gidan sa a siyasa, watau Bola Ahmad Tinubu.