Rahotanni sun bayyana cewa, Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ya kwanta rashin lafiya an garzaya dashi Asibiti a kasar waje.
Sahara Reports tace ta samu labari daga wata majiya a fadar shugaban kasa, cewa an garzaya da Akume zuwa kasar Jamus.
Zannan kwanansa biyar acan.
Akume dai bashi ke aikinsa ba, yana saka wasu ne suna masa kamar yanda majiyar ta bayyana.