Sojojin Najeriya sun sake kashe Boko Haram akalla 100 a Askira Uba dake jihar Borno.
Da yammacin yau, Laraba ne sojojin Najeriya suka kaddamar da harin bisa hadin kai da sojojin sama.
Sojojin sun lalata motocin yakin Boko Haram din da dama inda kuma suka kwace wasu da tarin makamai.