fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Da Duminsa:Wasu mata 2 sun tsere daga hannun Boko Haram

Wasu mata 2 sun samu tserewa daga hannun kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa.

 

Rundunar sojojin Najeriya ta Operation Hadin kai ce ta samu kubutar da matan bayan sun tsere.

Daya daga cikin matan sunanta Martha Yaga, ‘yar kimanin shekaru 19 da ‘yan Bindigar suka sace a Askira Uba shekaru 2 da suka gabata.

 

Sai kuma Blessing Adarju wadda itama shekarun ta 19, an sace ta a kauyen Kindindila dake jihar Adamawa.

 

Sunce sun kwashe awanni 7 suna gudu kamin su sami tsira, sunce Boko Haram ta aikasu neman abincine tare da wasu inda su suka tsere.

Leave a Reply

Your email address will not be published.