fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Da Duminsa:’Yan Bindiga sun kai hari Gwarimpa dake Abuja

Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa ‘yan Bindiga sun kai hari Gwarimpa dake cikin babban birnin tarayya Abuja.

 

Sun shiga ne da sassafiyar ranar Litinin inda suka kwashe mutane da dama suka tafi dasu.

 

Daily Trust tace da misalin karfe 1 zuwa 4 na darene aka kai harin wanda zuwa yanzu ba’a dan adadin mutanen da aka sace ba.

 

Kakakin ‘yansandan babban birnin tarayyar, Josephine Adeh tace lamarin ba na satar mutane bane, fashine aka yi kuma tace an kai jami’an tsaro wajan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.