Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya bayyana cewa, da gangan gwamnatin tarayya ta ki yin maganin matsalar tsaron da ake fama da ita.
Ya bayyana hakane yayin da wata kungiyar Turawa daga kasar Ingila suka kai masa ziyara.
Yace yana kira ga kungiyoyin Duniya dasu zo su sa gwamnatin tarayya ta magance matsalar tsaron da akw fama da ita ba tare da la’akari da banbancin Addini ko na kabila ba.
Ortom ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ta hannun sakataren yada labaransa, Nathaniel Ikyur.