fbpx
Thursday, February 9
Shadow

Da Maryam Sanda tayi irin wannan tunanin da bata kashe mijintaba:Karanta abinda wata mata tawa mijinta bayan ta ga sakon budurwashi

Wasu mutanen Allah yayi musu hikimar iya warware matsala ta hanya me sauki ba tare da kowa ma yasan me ya faruba, labarin wata matace a jihar Adamawa da ta kama mijinta yana hirar soyayya da wata budurwa a waje, taga sakonnin soyayyar da mijin nata da budurwarshi suka aikawa junanshu ta dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook.

Ta zauna abin ya isheta, tana ta takaici da tunanin yanda zata bullowa wannan lamari, can sai wata dabara ta fadomata.

Ta lallaba ta dauki wayar mijinnata ta kwashe duk sakonnin da mijin nata da budurwarshi suka aikawa junansu na soyayya.
Taje ta bude sabon dandalin sada zumunta a facebook da sunan namiji, ta aikawa mijinnata  da gayyatar abota, ba tare da yasan cewa itaceba kuma akayi sa’a ya amshi gayyatar abotan.
Bayan sun gaisa, sai ta gayamishi ni dan Boko Haramne kuma naga kana hirar soyayya da matata, ta gaya mishi sunanshi sannan tace , kuma inada duk sakonnin daka aikamata, ta aika mai da sakonnin nan data kwasa daga wayarshi.
Taci gaba dacemai, na sanka sosai, sunan matarka wance, kuma kana aiki a guri kaza, kana da ‘ya’ya wane da wane, kuma babban abokinka shine wane, ga inda kake hira kullun, saboda haka, ka kiyayi matata, karka sake aikomata da sakon soyayya, idan kuma ba hakaba to zan maka yankan rago.
Lokacin da yake karanta wannan sako matar tashi na kusa dashi, taji ya buga salati, tace lafiya?, yace mata babu komai.
Haka ya tashi yaje ya sayar da wayar a kasuwa ya siyo wata , daga nan bai karaba.
Babu tabbacin wanna labari ya faru, amma saboda hikimar dake cikinshi yasa aka bayar dashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  An Kama Wani Gardi Da Yake Shigar Mata Yana Damfarar Maza Kudade

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *