fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Da Trump ya tuntubi Gwamna Ganjuje da bai fadi zaben Amurka ba>>Ado Doguwa

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta Nijeriya Honarabul Alhassan Ado Doguwa, ya ce tsohon shugaban Amurka Donald Trump ba lallai ba ne ya fadi zabe idan da ya nemi taimakon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

 

Alassan Ado Doguwa, wanda ke wakiltar karamar hukumar Tudunwada/Doguwa ta jihar Kano, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta wallafa a ranar Laraba, yayin da yake yi wa yan jarida jawabi.

 

Ya kara da cewa“Idan aka duba, lokacin da alkaluman suka fara nuna Trump zai sha kaye, ya kamata ya yi ya kira Ganduje a waya, shi kuma Ganduje sai ya tura masa Murtala sulen Garo ko Alhassan Ado ko Kawu Sumaila ko dan majalisa Kabiru Rurum, da labarin ba zai kasance haka ba a yau”.

 

Sannan ya ce don haka, tafiyar Gwamna Ganduje su a gurinsu Jami’a ce.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *