fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Da yawan ministocina na da ƙwarewar da za su gaje ni>>Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ban-kwana da ministocinsa da suka ajiye aiki don yin takara a babban zaɓe mai zuwa na 2023.

Yayin jawabinsa, Buhari ya ce ya yi imani da yawa daga cikin ministocin na da ƙwarewar da za su iya gadar sa.

“Babu wata tantama idan aka samu shugaban ƙasa daga cikin ministocin nan za a ga cikakkiyar ƙwarewa da kuma tsabar aiki ga al’umma,” in ji shi. “Wannan na ɗaya daga cikin tarihin da za mu bar wa ‘yan Najeriya.”

A ranar Laraba ne Buhari ya umarci dukkan ministoci da shugabannin hukumomi da ma’aikatu masu son tsayawa takara a muƙamai daban-daban da su ajiye ayyukansu nan da ranar Litinin mai zuwa.

Karanta wannan  Hoto:Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya kaiwa Mamman Daura ziyarar kamun kafa dan APC ta bashi takarar shugaban kasa

Daga cikin ministocin da suka yi ban-kwana da shugaban a yau har da Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda rahotanni ke cewa zai yi takarar gwamna a jiharsa ta Kebbi.

Sauaran su ne: Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, Ministan Ƙwadago Chris Ngige, Ƙaramin Ministan Man Fetur Timpre Sylva, Ministan Neja Delta Godswill Akpabio, Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, Ministar Harkokin Mata Pauline Tallen.

Sai kuma: Ƙaramin Ministan Ma’adanai Uche Ogah, Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, Ƙaramin Ministan Neja Delta Tayo Alasoadura.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.