Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce cikin shekaru 4 kacal ‘yan Nijeriya za su manta da batun dauke wutar lantarki da zarar sun zabe shi a zaben dake tafe na 2023.
Tinubu, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce gwamnatinsa za yi aikin samar da megawatt 15,000 da za a rika rabarwa ga Jihohin kasar nan ta yadda wutar zata wadata a ringa samunta koyaushe ba daukewa awanni 24 cikin kwanaki 7 na mako.
Ya kuke kallon kalaman Tinubun game da samar da wuta a Nijeriya?