fbpx
Friday, July 1
Shadow

Dabbanci Ne A Kashe Mace Da ‘Ya’yanta Hudu Saboda Bambancin Kabila Da Na Addini>>Sarkin Musulmi

… na yi magana da Gwamnan Anambara kan lamarin, cewarsa

Daga Bashir Babandi Gumel

Shugaban Majalisar koli akan lamurran addinin musulunci a Najeriya mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa akan yadda kafafen sada zumunta na yanar gizo ke ruruta irin wadannan matsalolin.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo inda ya baiyana cewa abinda ya faru a jihar Anambara, abu ne na dabbanci kuma mummuna a yanke mace da ‘ya’yanta wadanda basu ji ba basu gani ba, wai saboda bambancin kabila ko addini, wannan abin yana nuna kamar muna yaki da juna ba a fagen daga ba a kafafen sada zumunta na yanar gizo, ina son ince idan har wannan abin haka yake, na yi magana da gwamnan jihar Anambara Charles Soludu da wasu jagororin yankin akan wannan batun kuma na gamsu da matakan da suke dauka na shawo kan tashe-tashen hankulan jama’a a yankin na gabacin Najeriya don mu zauna lafiya da juna, mu muna kula da duk wanda ya zo ya zauna cikin mu don haka muna son muma a kula da namu mutane dake zaune a wasu wurare”.

Leave a Reply

Your email address will not be published.