Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson, ya ce ba za a sayar da motocin da ke amfani da man dizal da man Fetur a kasar nan da shekarar 2030 ba.
Wannan shawarar a cewar BBC wani bangare ne na abin da Johnson ya kira “juyin juya halin masana’antu” don magance canjin yanayi da samar da ayyukan yi a masana’antu kamar makamashin nukiliya.