fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Daga kasar Afghanistan ake yo hayar ‘yan bindiga don su tayar da hankula al’ummar Najerjya, cewar Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari ranar litinin inda yace babu gwamnati a Najeriya tunda har ‘yan bindiga suka ce zasuyi garkuwa da Buhari da gwamnan Kaduna, El Rufa’i.

Gwamnan ya bayyana hakan ne biyo bayan sabon bideyon da ‘yan bindiga suka saki sun lallasa mutanen da sukayi garkuwa dasu a jirgin kasa na jihar Kaduna.

Wanda ‘yan bindigar suka ce kwanan nan zasu yi garkuwa da shugaba Buhari tare da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i.

Karanta wannan  Wani magidanci tare da yaronsa sun mutu a cikin wata rijiya a jihar Kano

Gwamna Orton ya gana da manema labarai ranar litinin inda yace masu daga kasar Afghanistan ake yo hayar ‘yan bindiga suna tayar da hankulan al’ummar Najeriya tare da Fulani.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.