fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Daga Liberia: Shugaba Buhari ya nemi kasashen najiyar Afrika suyi koyi da Najeriya su gudanar da zabe cikin limana ba tare da tauye hakkin kowa ba

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi kira ga kasashen dake yammacin nahiyar Afrika cewa su gudanar da zabe cikini limana.

Buhari ya bayyana hakan ne a kasar Liberia inda ya ziyarci kasar tare da sauran shuwagabanni domin taya kasar murnar zagayowar ranar samun ‘yanci karo na 175.

Inda yace shi a kasar shi ta Najeriya zabe ake yi na tsakani da Allah ba a tauyewa kowa hakkinsa.

Saboda haka suma yana fatan zasu yi hakan musamman kasashen da zasu gudanar da zabe tare dasu a shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.