Hukumar kula da safarar jirgin kasa ta Najeriya, NRC ta bayyana aniyar dakatar da ayyukan jigilar Fasinjoji a jirgin saman na Najeriya gaba daya daga nan zuwa Ranar Litinin.
Hakan na zuwane jim kadan bayan da aka gano karin mutane 10 dake dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 a Babban birnin tarayya,Abuja da kuma Legas.
Ranar 23 ga watan Maris kenan za’a daina jigilar fasinja ta Jirgin kasa a Najeriya.
A wani labarin me kama da wanna mun kawo muku cewa Gwamnatin tarayya ta rufe gaba dayan filayen jiragen sama