Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a yau ya kaddamar da sabon kamfanin NNPC Limited a babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban kasar ya kara da cewa ‘yan kasuwa sun saka hannun jarin biliyan 200 a sabon kamfanin.
Kuma daga yanzu yace kamfanin zai riga sanarwa kansa riba ba tare da tallafin gwamnati ba.
Sannan yanzu zai cigaba da aiki ne kamar kamfani mai zaman kansa ba ba tare da takura ba.