Babban malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga al’ummar jihar Kano kan su kwantar da hankalinsu kuma su yi hakuri bisa sauke Sarki Muhammadu Sanusi da gwamnatin jihar ta yi.
Malamin ya yi addu’ar Allah ya kawo sauki cikin lamarin kuma ya kiyaye mutane.
Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wa Sarki addu’ar Allah Ya sa wannan mataki ya zama alkhairi a gare shi
BBChausa.