fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Dakarun Najeriya sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Dakarun shirin sharan daji da ake kira FOREST SANITY sun ce sun yi artabu da ƴan bindiga a yankin Danmarke na ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara lokacin da suke sintiri a yankin.

Sanarwar da sojojin Najeriyar suka fitar a ranar Alhamis ta ce a lokacin artabun ƴan bindigan sun tsere suka bar maɓuyarsu da makamai, yayin da da dama daga cikin su suka samu raunin harbin bindiga.

Dakarun sun samu nasarar kuɓutar da mutum uku, da ƙwato bindigogi ƙirar AK47 guda biyar, da kuma babura 30.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *