fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Dakarun Najeriya sun kashe Boko Haram 9, sojoji 2 sun jikkata

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta kacacaka wasu mayakan Boko Haram da suka kaiwa tawagar soji harin kwatan bauna a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda suka kashe 9 daga cikin mayan kungiyar.

 

Me magana da yawun rundunar sojin, Kanal Sagir Musa ya bayyana cewa, sojojin sun yi nasarar kashe Boko Haram 9 tare da kwace motocin da aka girke bindiga me kakkabo jirgin sama 2.

 

A jiya dai Munji labarin yanda Wasu mayakan Boko Haram suka kaiwa sojoji dake Mainok hari inda aka ji cewa suna ta bata kashi.

Karanta wannan  Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta daga aiki bayan daya lallasa wani mutun da adda

 

Daily Post ta ruwaito cewa Rundunar sojin Operation lafiya dole ta bayyana cewa ta dakile harin na Mainok a karamar hukumar Kaga da Boko Haram din suka kai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.