fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Dakarun soji sun ceto wata dalibar Chibok da yaronta dan shekara hudu

Dakarun sojin Hadin Kai sun sako ceto wata dalibar Chibok tare da yaronta dan shekara hudu da wasu mata guda uku a hannun ‘yan ta’addan Boko Haram.

Sunan dalibar Chibok din Aisha Grema kuma itace daliba ta 11 cikin daliban dake hannun ‘yan ta’addan a shekarar 2021.

Dakarun sojin Hadin Kai sun ceto dalibar ne tare da sauran matan a ranar juma’ar data gabata kamar yadda suka bayyana a shafinsu na Facebook.

A watan Afrilu na shekarar 2014 ne ‘yan ta’addan Boko Haram sukayi garkuwa da dalibai mata guda 276 a makarantar sakandiri ta Chibok a jihar Borno.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.