Dakarun sojin Najeriya sunyi nasarar ceto mutane bakwai a hannun ‘yan bindigar karamar hukumar Birnin Gwari da kuma Chikun na jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro na jihar ne ya bayyana hakan, Samuel Aruwan inda yace sunyi nasarar ceto su ne bayan sunyi musayar wuta a tsakaninsu.
Yace ‘yan bindigar sun tsere cikin daji ne domin hukumar taci karfinsu, kuma mutanen da aka ceto sun hada da wata mata da yaranta guda hudu.