Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Bindiga 2 a jihar Taraba. Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa sojojin na Rundunar Operation Whirl Stroke sun samu bayananan sirri kan Harin da ‘yan Bindigar suka kai kauyen Logo dake jihar Benue.
Yace an tashi sojoji dan tunkarar wadannan mahara amma kamin su je sun gudu bayan kashe mutane 2 a kauyen.
TROOPS OF OPERATION WHIRL STROKE NEUTRALIZES NOTORIOUS ARMED BANDITS IN ARUFU COMMUNITY OF TARABA STATE pic.twitter.com/ZWN9KGOUdb
— DEFENCE HQ NIGERIA (@DefenceInfoNG) July 11, 2020
Sojojin sun bi sahun Barayin inda suka iskesu a Arufu, jijar Taraba suka kuma kashe 2 daga ciki, wasu suka gudu da raunuka.