fbpx
Monday, June 27
Shadow

Dakarun Sojojin Saman Nijeriya Sun Yi Babbar Nasara Akan ‘Yan Boko Haram

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Dakarun Sojojin saman Nijeriya sun yi aman wuta akan ‘yan ta’addan Boko Haram.

Dakarun sojojin sama na Operation Hadin Kai sun kai samame ga yan ta’addan Boko Haram da tawagar yan ta’addan ISWAP tare da sheke tarin ‘yan ta’addan a wata musayar wuta a Borno.

Wata babbar majiyar sirri ce ta bayyana hakan ga Zagazola Makama, wani shahararren mai rahoton lamurran ta’addanci a yankin tafkin Chadi.

A cewar majiyar, misalin karfe 1:30 na dare, tawagar’yan ta’addan ta nufi Wara Wara – don birne gawawwakin yan ta’addan ISWAP din da aka sheke gami da yi musu sallar jana’iza.

Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa a karshen makon nan ne, dakarun sojin sama na Operation Hadin Kai suka kai wa ‘yan Boko Haram da ISWAP samame inda suka sheke tarin ‘yan ta’adda da dama yayin wani farmaki a jirgin sama a arewa maso gabacin Borno, Zagazola ya tabbatar.

Majiyoyin sun labarta yadda aka yi nasara a samamen da aka kai a ranar 21 ga watan Mayu a Wara Wara – wani kauye a karamar hukumar Damboa.

Karanta wannan  Babban dalilin dayasa Najeriya ke cigaba da kasancewa kasa mafi talauci a fadin duniya

Majiyar ta kara da bayyana yadda ta cigaba da dauko jiragen yakin sama don ganin an ragargaji hatsabiban, luguden wutar ya yi nasarar sheke wata tawagar hatsabiban.

Yayin cigaba da bayani, majiyar ta ce luguden wutar da aka aiwatar da taimakon Operation Desert Sanity, bayan tarin binciken da ya nuna ayyukan ‘yan ta’adda wuraren Korede, Shettim Affor, kauyen Kalolowa da kauyen Wara Wara dake Damboa ya haifar da abinda ake so.

Shahararren mai binciken sirri da lura da lamurran ta’addanci a tafkin Cadi, Zagazola Makama ya tabbatar da yadda samamen ya gabata inda ya ce jiragen saman yakin sun kai farmaki gami da tarwatsa motocin bindiga hudu tare da halaka yan ta’addan da dama yayin kai harin.

Muna rokon ubangiji Allah ya azurta kasar mu Nijeriya da zaman lafiya mai daurewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.