fbpx
Monday, March 1
Shadow

Dakta Zahra’u tayi kira da jahohin dake da Makwaftaka da jihar Kano da su daina barin Al’majiarai daga jahohin su suna kwararowa cikin jihar

Kwamishiyar Mata ta Jihar Kano Dakta Malama Zahra’u Umar ta yi kira Da Makwaftan Jahohin dake da kusanci da Jihar Kano da su daina barin Al’majirai daga yan kunanan su suna cigaba da kwaranya cikin jihar.

Dakta Zahra’u tayi wannan kiran ne a jihar, Inda ta danganta bazuwar Al’majirai cikin jihar a matsayin barazana ta fuskar tsaro.
A cewarta Gwamnatin jihar Kano Bazata zuba idano tana ganin Al’majiari daga ko wanne sassa suna shigowa kano ba.
Datake yin kira Da sauran Jahohin da Al’majiran ke fitowa ta ce Galibin su suna fitowa ne daga jahohin Katsina Da kuma Kaduna inda tai kira da Gwamnonin jahohin da su dauki Matakin da jihar kano ta Dauka na mayar da Al’majiran zuwa ga Makusantan su tare da basu horo kan Sana’o’i domin suma su dogara da Kansu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *