Kungiyar daliban Najeriya reshen jihar Osun sun roki kungiyar malaman jami’a ta ASUU da gwamnatin tarayya da su yi sulhu.
Daliban sun koka da yajin aikin da ASUU ke yi inda suka yi rokon a bi hanyar sulhu dan warware matsalar.
Yajin aikin da a yanzu ya kai kwanaki 60 daliban sun ce ya fara damunsu saboda basu san randa zasu koma makaranta ba.
Kungiyar tace idan da gwamnati ta damu da yanayin da ilimi ke ciki na lalacewa a Najeriya, ya kamata ta aiwatar da shawarwarin da Alkawuran da suka yi da ASUU.
Kungiyar tace tasha zuwa yanzu gwamnatin zata dauki matakin gyara a lamarin, amma gashi yanzu har an kwana 60 babu wata alamar cewa gwamnatin zata magance matsalar.
Kungiyar tace muddin ba’a kawo karshen lamarin ba, ba zata yi shiru ba zata ci gaba da fafutukar ganin an dauki mataki.