fbpx
Monday, August 15
Shadow

Daliban jihar Edo dake zama a kasa suna koyan karatu sun nemi agajin gaggawa daga wurin gwamnati

Al’ummar Ofunmwegbe dake kudu maso kudancin jihar Edo sunyi kira ga gwamnati cewa ta dubi halin da yara ke ciki ta gyara masu makaranta daya tilo dake yankin.

Inda suka bayyana cewa makarantar ta lalace sosai don ba katangan wanda ke kebawa ‘yan bindiga damar shiga a duk sanda sukaga dama.

Sannan rufin makarantar duk ya lalace sannan kujeru sunyi karanci dalibai a kasa suke zama ana koyar da su karatu kuma malamai sun yi karanci a makarantar.

Sun kara da cewa shima kasan da daliban ke zama a lalace yake kuma hakan yasa iyaye sun fara cire yaransu a makarantar, saboda suna kira ga gwamnati ta kawo masu agajin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.