fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Daliban makarantar al-qur’ani 2 sun mutu sakamakon rugujewar gini a Kano

Rahotanni sun ce dalibai biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu uku suka samu raunuka bayan wani gini da ba’a kammala ba da ke unguwar Hotoro, da ake kira Hotoro Unguwar Gabas, a bayan tashar Chula, ya ruguje da misalin karfe 3 na safiyar ranar Juma’a 8 ga watan Afrilu.

Rahotanni sun bayyana cewa ginin da bai kammala ba yana kusa da wata makarantar kur’ani mai tsarki (makarantar allo) inda daliban makarantar su biyar ke kwana.

A cikin daren nan, biyu daga cikin daliban biyar sun mutu yayin da sauran suka samu munanan raunuka bayan ginin ya rufta musu.

Karanta wannan  Najeriya zata iya lalacewa idan kuka cigaba da sukar mulkina, cewar shugaba Buhari

Daliban da suka mutu su ne Ali mai shekara 28 da kuma Abdulganiyu mai kimanin shekara 22,” in ji wani ganau.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.