Daliban makarantun gwamnati a jihar Zamfara sun daina zuwa makaranta koyon karatu kan gwmnatin jihar ta daina basu abincin tallafi.
Bashin da gwamnatin jihar ke ciyowa kan ciyar da daliban makarantun gwamnati a jihar yayi yawa sosai,
Kuma hakan ne yasa gwamnatin ta dakatar da basu wannan abincin na tallafi a makarantunsu.
Kuma shugaban wata makaranta a jihar wanda bai bayyana sunansa ba yace wannan abin yasa yawancin yara sun daina zuwa makarantu koyon karatu.
Kuma rashin zuwa nasu makaranti babban kalubale ga cigaba ilimin zamani a jihar dama kasa bakidaya.