Ɗalibin Abdulrazak Nafi’u Abubukar, Dan Shekara 27 Da Haihuwa Dan Asalin Karamar Hukumar Nasarawa A Jihar Kano Ya Yi Zarra Inda Ya Samu CGPA 9.89 Cikin 10.00 A Jami’ar Sharda Dake Ƙasar Indiya. Inda Aka Karrama Shi Da Kambu Zinari Na Mataimakin Shugaban Jami’ar A Digirinsa Na Biyu Kan (Technology In Engineering)
Ya Karantu A Jami’ar Bayero Da Ke Kano, Inda Ya Karanta(Mechatronics Engineering) A Digirinsa Na Farko.

Gidauniyar Tsohan Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso Watau (Kwankwasiyya Development Foundation) Ta Dauki Dawainiyar Karatunsa Zuwa Ƙasar India.
Daga Jamilu Dabawa, Katsina