Dalibin makarantar Polytechnic ta jihar Legas wato YABATECH ya mutu a ranar juma’a yayin da suke sharholiyar kammala makaranta.
Kungiyar daliban makarantar ce ta tabbatar da wannan labarin inda kuma shine kadai yaron a wurin iyayensa.
Abraham ya mutu ne bayan daya fado daga motarsu wadda suke saka kida a ciki suke sharholiyarsu.
Kuma Abraham ya kasance dalibin sashen karatun Computer Engineering.