fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Dalilin da yasa gwamnoni da yawa ba zasu iya yaki da Coronavirus/COVID-19 ba>>Hakeem Baba Ahmad

Tsohon babban darakta a hukumar zabe me zaman kanta, INEC kuma hadimin tsohon kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa da yawan gwamnonin Najeriya na zasu iya yaki da Coronavirus/COVID-19 ba saboda basu da isassun kayan aiki.

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Sun inda yace rashin wadannan isassun kayan aiki ko kudi ne yasa gwamnonin ba zasu iya tsare mutane a gida ba ta yanda ba zasu kai kansu ga inda zasu samu cutar ba.

Ya kara da cewa su kuma mutane yawanci basu damu da kansu ba kuma suna ganin wannan cuta kawai ba ta da wata muhummanci. Ya kara da cewa watakila lokacin da mutane zasu dauki cutar da muhimmanci sai an fara ganin dubban mutane na mutuwa tukuna.

Karanta wannan  Mutane 12 sun mutu a musayar wutar da 'yan bindiga suka yi da vigilanti a jihar Filato

 

Yace gashi yanzu ma gwamnatin tarayya ta mikawa gwamnatocin jihohi yaki da cutar. Watakila nan gaba su kuma gwamnatocin jihohi su mikawa kananan hukumomi.

 

Yanzu dai Najeriya nada mutane 12,233 da suka kamu da cutar sannan kuma 3,826 sun warke sai 342 da suka mutu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.