fbpx
Friday, May 27
Shadow

Dalilin da yasa har yanzu bamu fara neman shuwagabannin ‘yan Bindiga ruwa a jallo ba kuma bamu bayyana hotunansu ga ‘yan Najeriya ba>>Sojojin Nigeria

Hukumar sojojin Najeriya ta bayyana dalilin da yasa bata neman Shuwagabannin ‘yan Bindiga ruwa a jallo.

 

A lokacin tsohon shugaban kungiyar Boko Haram watau Abubakar Shekau ke raye, an wallafa hotunansa da mayakansa inda ake nemansu ruwa a jallo.

 

Shin ko me yasa ba’a wa ‘yan Bindiga irin wannan abuba?

 

Kakakin Hedikwatar tsaron Najeriya, Benard Onyeuko ya bayyana cewa, suna kan kokarin ganin an wallafa hotunan Shuwagabannin ‘yan Bindigar kuma a fara nemansu ruwa a jallo.

 

Yace suna kan tantancewane shiyasa har yanzu basu bayyanawa ‘yan Najeriya suba, amma nan gaba kadan za’a jisu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.